Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sepp Blatter da Michel Platini Sun Ce Zasu Daukaka Karar Dakatarwar Shekaru 8


Sepp Blatter (dama) da Michel Platini
Sepp Blatter (dama) da Michel Platini

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta bayar da sanarwar dakatar da jigoginta Sepp Blatter da Michel Platini nan take daga duk wata harkar kwallon kafa har na tsawon shekaru 8.

Kwamitin da’a na hukumar ta FIFA ya gudanar da binciken mutanen biyu dangane da wani kudin da Sepp Blatter ya biya Michel Platini a watan Fabrairun 2011, kudin da aka ce ya saba ka’ida.

Kwamitin da’ar yace bai gamsu da bayanin da Platini yayi na dalili ko dalilan biyansa wannan kudi ba, don haka zai biya tarar Franc dubu 80 na kudin kasar Switzerland, yayin da Blatter zai biya tarar dubu 50. Kudin na Switzerland kusan daidai yake da dalar Amurka a daraja.

Dukkan mutanen biyu sun lashi takobin daukaka kara.

Wata sanarwar da hukumnar FIFA ta bayar ta ce, “Binciken da aka gudanar game da Blatter ya fi mayarda hankali ne kan kudi Franc miliyan biyu, kimanin dala miliyan biyu, da aka cire daga aljihun FIFA aka biya Platini a watan Fabrairu na 2011. Mr. Blatter, a matsayinsa na shugaban hukumar FIFA, ya amince da a biya Platini wannan kudi wand aba ya bisa wata ka’ida ta shari’a idan aka duba cikin yarjejeniyar da mutanen biyu suka sanya ma hannu a ranar 25 ga watan Agustar 1999. A cikin jawabinsa na kariya da ya bayar a rubuce, da kuma shaidar da ya bayar da kansa, Mr. Blatter ya kasa bayyana wata hujjar shari’a ta biyan wannan kudin. Dalilan da ya bayar cewa ya biya wannan kudin ne bisa yarjejeniyar baka, ba rubutacciya ba, ba ta gamsar ba, don haka kwamitin da’ar bai amince da wannan ba.”

XS
SM
MD
LG