Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FIFA Ta Ce Ta Yi Kuskure Wajan Bada Wata Lambar Yabo A Wasan U-17


Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta bayyana cewa a bisa kuskure ne ta ba Kelechi Nwakali lambar yabo a wasan cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 a maimakon takwaransa Samuel Chukwueze.

Chukwueze ya jefa kwallaye a cikin mintuna (535) ne shi kuma Nwakali ya jefa nasa ne a cikin mintuna (630) kuma duka ‘yan wasan biyu sun jefa kwallaye uku uku ne, kuma sun bada gagarumin taimako wajan ganin sun sami nasarar lashe wasan.

Ko da shike hukumar FIFA ta fitar da sunan Nwakali a matsayin na uku cikin wadanda suka fi kowa jefa kwallo a raga, duk da sauran kokarin da dan wasan ya yi.

“Mun yi kuskure ne a wajan bukin kammala wasan hukumat FIFA na cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 wajan rarraba lambar yabo ta Bronze Boot, a wata kasida da hukumar FIFA ta aika wa hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya.

A maimakon dan wasan Najeriya mai lamba 8, Samuel Chukwueze, Kelechi Nwakali mai lamba 10 ya amshi kyautar takalmin Bronze, saboda haka idan ‘yan wasa biyu suka taka rawar gani bayan jefa kwallaye a raga da kuma bada kokari wajan samar wa da kungiyar su nasara, dole ne dan wasan da yake da mintoci kadan ya fara karbar lambar yabo.

A sakamakon haka, kanfanin Adidas zai aikawa da Samuel Chukwueze takalmin Bronze a awannan watan na disamba wanda ya kamata ya amsa tun farko.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG