Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Budurwar Data Gaza Samun Saurayin Kirki?


Boy Friend
Boy Friend

Duk wata mace da ta gagara samun miji, to lallai akwai abun dubawa a kanta. A matsayin ki na mace kin taba kokarin samun na mijin kirki amma baki samu ba? Ga wasu shawar’wari daga bakin masana. Idan har duk yadda ki kayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma ya damu da ke, amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki.

Ke mace ce mai tsiwa, fada da kowa, rashin kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi? To fara duba kanki ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadda sauran mutane, ke gudanar da rayuwar su ta halin yau da kullun? Yima kanki adalci wajen bayyanar ma kanki da gaskiya koda kuwa baza kiji dadin yin hakan ba.

Ke maccen cikin gida ce? Baki zuwa makaranta, baki da kawaye da suke zuwa makaranta, kuma duk samarin unguwar ku sun sanki, fara neman saurayi dan wata anguwa ko wani gari, hakan kuma na iya kasancewa ne idan kika ziyarci kawaye da suke wasu anguwa, kuma suke mu’amala da mutane kirki. Daga nan sai kiji amfara tambayar wai ina kawarki ta anguwa kaza? Haka kuma kin iya girki kuwa? Kokarta wajen karanta littatafai da ake koyar da girke-girken zamani, don koya ma kawayen ki da suke da samari da mazajen kirki, daga nan abokan miji zasu fara sanar da abokan su, cewar kawar matata ta koya ma matata yadda ake yin abinci kaza, kinga daga nan hanya ta budu.

Ya kuka gani? Ku rubuto muna naku ganin a shafinmu na facebook.com/voahausa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG