Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana'ar Waka Sana'ar Nuna Basira Da Baiwa


Ishaq Tasiu Nasidi
Ishaq Tasiu Nasidi

Wani mawakin Kannywood, Ishaq Tasiu Nasidi, yace sana’ar waka sana’ar ce da take baiwa mutun damar nuna basira da baiwar da Allah ya yiwa mawakin.

Ya bayyana haka ne a hira da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir. Yana mai cewa yana wakokin domin tallata hajja na masu kananan sana’oin domin su zamo masu dogaro da kai tare da inganta kasuwancin da suke yi.

Ishaq Tasiu Nasidi wanda aka fi sani da Istanas ya ce yana waka ne da manufar fadakar da jama’a da kuma wa’azantar dasu baya ga tallata hajja da yake wa masu kananan sana’oi, abinda yace ya samu Karin horarwa akai a lokacin da ya hallarci wani taron masu kananan sana’oi.

Istanas ya kara da cewa yana yiwa masu fina-finai wakokin da aka sanya a wasu fina-finan sannan yana yiwa wasu daga cikin ‘yan siyasa, amma yana yin kwakkwaran bincike akan dan siyasan gudan kada ya fadi abinda ba shi ne ba.

Ya ce a hannu guda banda waka yana tallace-tallace idan hali ya samu na dukkanin kaya muddin dai akwai muradin a sayar da kayan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG