Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamshakin Mai Kudi Yarima Alwaleed Da Wasu Zasu Fuskanci Shari'a


Yarima Al-Waleed bin Talal
Yarima Al-Waleed bin Talal

A jiya Lahadi ne hukumomi a kasar Saudi Arabiya, suka bada umurnin kama wasu ‘yan sarauta goma sha biyu, tare da wasu tsofaffin ministoci. Wanda suka hada da hamshakin mai kudin kasar Yarima Alwaleed. Duk a wani bincike da ake gudanarwa na cin hanci da rashawa.

Hakan na faruwa ne a karkashin sarautar Sarki Salman tare da yariman shi, a tabakin daya daga cikin manya ma’aikatan kamfanin “Prince Alwaleed bin Talal’s Kingdom Holding Company” an samu nasarar tsare manya manyan mutane a daren Asabar.

A jiya Lahadi kuwa kasuwar hannun jari a kasar ta Saudi Arabiya ta fadi da kashi 1.5% mintoci kadan da bude kasuwar. Yarima Alwaleed, na daya daga cikin hamshakan masu kudi a baki daya kasashen daular Larabawa.

Yana da hannun jari a kamfanonin kasashen duniya, da suka hada da kamfanin Twitter, Apple, Rupert Murdoch, Citigroup da dai sauran manyan kamfanoni, haka kuma yana da hannun jari a kamfanin Uber a ko’ina a duniya.

Yarima Alwaleed, hamshakin mai kudi na daya daga cikin masu magana a madadin gwamnatin kasar, kuma tsohon dan rajin kare hakkin mata ne a kasar ta Saudiya.

Gidan talabijin na kasar Saudiyya Al-Arabiya, sun tabbatar da kamen, da ya hada da ‘yayan sarki goma sha daya, da tsofaffin ministoci goma sha biyu. Hakan yayi dai-dai da shari’ar Islama na ganin an hukunta duk wanda yayi ta’anati da dukiyar kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG