Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakonnin Sallah Daga Masu Sauraro


Ga gaisuwar sallah daga ‘yan uwa da abokan arzuki a masallacin eid na masallacin BUK da ke kan titin Gwarzo jihar Kano, Najeriya.

Mafi yawa daga cikin wadanda suka mika sakon gaisuwar su, Malama Amina Mika’ilu Aliyu wadda ta ce tana godewa Allah da ya nuna mata ranar karamar sallah tana mai fatan Allah ya zaunar da Najeriya, lafiya ya kuma jikan iyaye da kakanni tare da mika goron gaisuwar sallah ga ‘yan uwa da abokan arziki tare da gaida iyayenta da ‘ya’yanta khadija Kursi da Aliyu.

Ita kuwa Aisha Umar Aliyu cewa ta yi Allah ya maimaita ya karbi ibadunmu,

Safiya, kuwa cewa ta yi tana farin Ciki tare da gaida ‘yan uwa da abokan arziki tare da fatan Allah ya maimaita mana.

Zainab, ta ce rana ce ta farin cikin tana gaida iyayenta da mai gidanta da dukkanin musulmai a fadin duniya.

Umar Sani Isa ya ce yana gaida babarsa da babansa da fatan Allah ya maimaita mana.

Dukansu dai na farin cikin samun sallah karama cikin koshin lafiya tare da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Saurari sakonnin gaishe gaishen a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG