Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wankin Kai Da Kunshi Domin Fitowa Shar A Ranar Sallah


A yayin da ake sauran kwanaki kadan ga sallah karama tuni ‘yan mata da matan aure suka fara tururuwa zuwa gidajen wankin kai da kunshi domin fitowa shar da su a safiyar sallah karama.

DandalinVOA ya samu zantawa da Malama Zinatu wacce ta ce ta zo gidan wankin kai ne domin a yi mata Karin gashi duk don tarar bukukuwan sallah a cewarta domin ta birge mijinta a lokacin sallah duk kuwa da cewar a duk sati take kitso da yake amma da shike sallah ce ana yi mata karin gashi domin ta fito a safiyar sallah.

Khadija A Abubakar, kuwa cewa ta yi ta zo wash and set ne saboda karatowar bikin sallah karama kuma zata je amsar kayan sallah da ke wajen tela kuma daga nan zata je ayi mata kitso.

Sadiya Saminu, ita ma kamar sauran yara ta ce ta zo ne domin yin kitson sallah don ta sami damar zuwa kallon hawan sarki. Fatima Ahmad kamar kowa ta ce ta zo a wanke mata gashi ne domin karatowar bukukuwan sallah, bayan nan zata je ayi mata kitso da kumshi.

Daga karshe malama Hafsa Sabitu, mai gyaran gashi ta ce tun kwanaki uku da suka gataba ta fara samun cunkoson mutane duk don sallah karama ta ce tuni suka fara bude shagon tun sanyin safiya kuma suna jimawa a saloon din domin gyarawa mata gashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:32 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG