Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Hanyar Magance Sankaran Mama Ba Batare Da Chemo Ba


Ta yiwu yawancin matan da aka gano suna da cutar sankaran mama a matakin farko-farko, su iya kaucewa jinyar yin amfani da hade-haden magunguna dabam dabam da ake kira Chemotherapy, a cewar wani bincike.

Binciken da aka wallafa jiya Lahadi a mujallar New England Journal of Medicine, wanda Dr. Joseph Sparano ya jagoranta, ya gano cewar matan da aka gano suna da wani kumburi wanda bai yadu zuwa wasu wuraren ba, sun sami sauki ta shan magunguna kusan kamar wadanda suka yi jinyar Chemotherapy.

Binciken, wanda shine mafi girma da aka taba yi akan maganin sankaran mama, zai iya cetar mata Amurkawa kusan 70,000 daga yin amfani da Chemotherapy a kowacce shekara.

Binciken ya kuma gano cewa wani gwajin kwayar hallita da ake yiwa kumburin (a mama) zai iya gano macen da za ta iya shan maganin da zai toshe sinadarin mata da ake kira Estrogen, ko ya hana jikin mace yin sinadarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG