Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Ya Mutum Zai Canza Sharrin Da Ya Sameshi Zuwa Alheri?


Ali Banat
Ali Banat

Labarin wani matashin da ya mayar da kamuwa da cutar cancer alheri

Ali Banat wani matashi ne dan kasuwa mazaunin Australia da ya samu nasarar yin arzikin da babu abin da ya rasa a rayuwarsa. Sai dai kash! A shekarar 2015, Likitoci suka sanar da shi cewa ya kamu da cutar sankara wato cancer a turance, sannan ta yi tsamarin da ba za a iya yin magani ba. Kuma tun lokacin Likitocin sun yi hasashen cewa ba zai wuce watanni 7 a duniya ba.

Idan kai ne ya zaka yi in aka cewa maka saura maka watanni 7 kacal a duniya? A wata hira da yayi da One Path Network, ya bayyana cewa, “kamuwa da cutar cancer alheri ce a gareni domin wata dama ce da Allah ya bani domin in canza rayuwata kwata-kwata.”

Daga nan ne, Ali ya zabura domin kyautata makomarsa, inda ya kyautar da duk abubuwan da ya mallaka kamar motoci masu tsada irin Ferrari, da agoguna na kusan dala dubu 60 da sauransu. Akasarin kyautar tasa a Afirka ta kasance.

“Wallahi abin duniya duk ya fita daga raina, idan har aka sanar da kai cewa kwanakinka ragaggu ne, to duk wadannan abubuwan ba za ka yi tunaninsu ba,” inji Ali

A Oktobar 2015 ne ya kafa wata kungiyar Musulman duniya ‘Muslims Around The World Project” da nufin tallafawa marasa galihu musamman a kasar Togo inda suka samarwa mata 200 da suka rasa mazajensu gidajen zama kyauta. Suka kuma gina masallaci da makarantar marayu da karamin asibiti da sauransu.

(Wata makaranta da kungiyar ke tallafawa a Togo)

“Na kafa wannan kungiyar ne bayan da na gane cewa babu abin da mutum zai tafi da shi lahira face ayyukansa, duk dukiyar da ka mallaka duk a duniya za ka barta”.

(Taimakon azumi da suka samar a Togo)

Allah sarki duniya, a yau din nan ranar 29 ga watan Mayu 2018 da muke ciki, kuma a cikin watan nan na azumin Ramadan, Ali Banat ya koma ga Mahaliccinsa, bayan da ya zarce wa’adin da likitoci suka diba masa da shekaru biyu har da watanni.

(Bidiyonsa na karshe da aka saka a kafofin sadarwa)

​Allah ya jikansa da rahama ya kuma kyautata namu karshen.

Tambaya: Wane aikin alheri ka yi ko kuma kake kan yi don kyautata makomarka?

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG