Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani shahararren kamfani mai mazauni a jihar California ta Amurka “Boring Company” na gab da kammala shirin sa na sufuri wanda zai iya daukar motar matafiyi don kai shi wani gari, tsarin wanda aka shirya a cikin karkashin kasa mai kimanin kilomita 3.2 cikin zurfin kasa.

Shirin zai dauki mutun da motar sa, kuma yana gudun famfalaki wanda hakan zai kawo karshen matsalar cinkoson ababen hawa a cikin manya manyan garuruwa.

Za'a fara gwajin sabon tsarin a jihar ta California, kamfanin wanda yake daya daga cikin bangaren kamfanin Tesla masu kera motoci masu amfani da hasken rana na kasar Amurka, da jirgin nan mai shiga cikin sararrin samaniya na SpaceX.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG