Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rohit Shetty Yafi Samun Daukaka Ta Musamman A Bollywood


Rohit Shetty Bollywood
Rohit Shetty Bollywood

Rohit Shetty, ya kasance fitatcen mai bada umarin a Bollywood, ganin cewa duk fina finan da ya bada umarni akan a bana dai, a Bollywood, sun taka rawar gani ta inda suka samar da makudan kudade abinda yasa ake masa lakabi da mai kashin arziki.

Tunda fitowar fim din Golmaal 3, ganin irin alherin da fim din ya samu biyo bayan karbuwar da fim din yayi a tsakanin ma’abota kallon fina finai, linzaminsa sai gaba gaba yake yi a faggen fina finai.

Kusan duk shekara idan Rohit Shetty, ya bada umarni a fitar da fim to tabbaci hakika wannan fim din zai kasance ya shiga zukatan mutane sosai kuma ya samarda dimbin kudade.

Fina finan da Rohit Shetty, ya bada umarni akan su kuma suka samarda makudan kudaden sun hada da Golmaal, Singham, Chennai Express, Singham Returns, Bol Bachchan, Dilwale da kuma Golmaal a karo na biyu.

Fina finan Rohit Shetty, su kasance masu sabbin dabaru da kyalkyali a ko da wane lokaci shi yasa ma’abota kallon fina finai ke sha’awar fina finan Shetty, kuma akaro na biyu fim din Golmaal, a cikin kwanaki tara kacal ya samarda kimani dalar Amurka miliyan talatin da biyu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG