Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Perisic Ya Koma Bayern Munich A Matsayin Aro


Ivan Perisic

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta dauki dan wasan gefe na klub din Inter Millan kuma dan kasar Croatia, Ivan Perisic a matsayin aro a yarjejeniyar shekara daya, a cewar klub din a yau Talata.

Darakta mai kula da wasanni na klub din Bayern Munich, Hasan Salihamidzic, ya ce Ivan zai taimakawa kungiyar saboda irin gogewarsa na buga wasannin kasa da kasa.

Bayern ta na duba yiwuwar sabon dan wasan ya zama mata wanda zai maye gurbin dan wasan Manchester City, Leroy Sane, da ya samu rauni a gwiwarsa kwanannan, bayan da ta yi yunkurin dakko shi.

Dan wasan ya tabbatarwa da kafofin yada labarai na Jamani komawarsa bayan da aka hange shi ana duba lafiyarsa a Birnin Munich a jiya Litinin.

A cewar jaridar Bild, kulab din Bayern Munich ya biya dala ($6,257,048) akan dan wasan na kasar Croatia, tare da yiwuwar za ta siye shi nan gaba akan kudi da yakai kusan dala ($22,346,600) zuwa karshen kakar wasanni nan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG