Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nishadi Tare Da Mustapha J T


Nishadi Tare Da Mustapha J T
Nishadi Tare Da Mustapha J T

A shirinmu na nishadi a yau dandali ya samu bakuncin wani mawaki Mustapha Adam wanda aka fi sani da Mustapha J T wanda ya shafe shekaru takwas yana harkar waka

Ko da yake harkar fim ya fara daga bisani ya tsunduma a harkar waka, ya ce sha’awa ce ta ja shi ga waka , ya kuma kara da cewa yanayin rayuwar da ake ciki a yanzu sai mutum ya zama ya iya abubuwa da dama , domin kuwa har kawo yanzu idan ya samu damar zai yi fim

Ya ce yana harkar wakokin sa ne da kayan zamani saboda cigaban rayuwa

Burin Mustapha J T dai shine wakar sa ta yi tasiri ga al’umma sannan ya na aduar mutane su fahimci abinda wakarsa ta kunsa

A fannin tsegumi kuwa bayan dawowar Ali Nuhu daga kasar Nijar , jarumin ya karasa wani aikin fim dinsa mai suna SADAUKI a garin kano ko da yake ana tunanin sauya wa shirin suna sakamakon karo da yayi da wani shirin

Alin dai ya wuce garin Jos bisa gayyatarsa da wani kamfani na 3 SP yayi damin gudanar da wani sabon aiki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG