Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Fasaha Na Kawo Mata Cikas a Sana’arta


A rahotonmu na mata a yau mun sami zantawa ne da wata matashiya mai sana’ar tallace-tallacen da ake sawa a gidajen rediyo.

zainab Abdulrahman ta ce ta fara wannan sana’a na ta ne shekaru goma da suka wuce , sakamakon yawan mu’amala da ta ke yi da ma’aikatan gidajen rediyo.

Ta fara wannan sana’a ne bayan da ta ci wani biscuit da yayi mata dadi ta kuma dubu yadda ta ke jin tallace tallacen abubawa a rediyo sai ita ma ta rubuta ta yi tallan ba tare da kamfanin biscuit din sun sani ba ,daga bisani kwatsam sai ga wani kamfani ya kawo mata talla.

Ta ce abinda ya ke ci mata tuwo a kwara dai bai wuce yadda ake yi mata satar fasaha ba da zarar ta yi tallan wani abu sai ta ji an sata an juya anyi wani tallan da shi.

Burinta kuwa shine ta bude babban kamfani da za ta rinka yin tallunka a nan gida da ma kasahne waje.

XS
SM
MD
LG