Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ni Da Kaina Naki Zuwa Real Madrid (Pogba)


Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa mai taka leda a kungirar kwallon kafa ta Manchester United, kuma dan wasan da yafi kowane dan wasa tsada a duniya bangaren tamola Paul Pogba, ya ce shi da kansa yake amincewa da yaje kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ko kuma Barcelona.

Pogba ya ce badan komaiba sai don yana so ya dawo tsohowar kungiyar ta Manchester united, domin yanada wasu burinsa da yake so yacika a Kungiyar, daya daga cikin burinsa shine ya samu nasarar lashe wani babban kofi a kungiyar don haka shi badan kudi yazo Manchester united ba.

Kungiyar ta Manchester, dai ta sayi dan wasan daga kungiyar kwallon kafa ta Juventus, a kan zunzurutun kudi har fam miliyan £89, a farkon kakar wasan Bana 2016/2017, wanda a baya Manchester, ta sake shi ya tafi Juventus, a matsayin kyauta a shekara ta 2012.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG