Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atonio Conte Ya Gargadi Diego Costa Kada Ya Biyewa Kudi


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Diego Costa na iya barin kungiyar domin komawa wata Kungiyar kwallon kafa a kasar China a karshen kakanr wasan bana.

Sai dai mai horas da kungiyar ta Chelsea, Antonio Conte, ya gargadi dan wasan da kar ya biye wa kudi ya kamata ya kare mutuncin sa ya cigaba da zama a babbar kungiyarsa ta Chelsea

A sati biyu da suka wuce ne dai kungiyar ta Chelsea ta sayar da ‘yan wasanta har guda biyu ga wata kungiyar kwallon kafa ta kasar China, ‘yan wasan sune Oscar da Mikel Obi.

Arjen Robben na Bayern Munich, ya ce sun cinma matsaya da kulob dinsa na tsawaita kwantirakinsa zuwa shekara ta dubu biyu da Goma Sha takwas.

Monaco, ta ki amincewa da tayin fam miliyan £45 da wata kungiya a kasar China ta yi wa dan wasanta mai suna Radamel Falcao. Shima dan wasan Crystal palace, Cristian Benteke, yace baya da sha'awar barin kungiyarsa domin komawa PSG.

Dan wasan gaba na kasar Gabon mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Emerick Aubameyang, ya ce yana matukar jin dadin zamansa a kungiyarsa ta Dortmund, don haka bazai koma Real Madrid ko Barcelona ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG