Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Fi Maida Hankali Wajen Wake Jihata - Aminu Genius


A Fannin Nishadi yau, Dandalinvoa ya samu zantawa da wani matashi mai suna Aminu Haruna wanda ke wakokin hip-hop amma amfi sanin sa da suna Genius.

A wata hira da Baraka Bashir, Genius ya fadi cewa a yanzu yafi mai da hankali ne wajen wake asalin sa wato Jihar Jigawa domin duniya ta santa da irin Albarkatun da take dasu.

Genius, mawakin hip hop da Afro pop wanda yace sha’awa ce, ta jashi ga harkar waka tun yana makarantar sakandare a irin kungiyoyin nan da ake kafawa na nishadi, daga nan ne ya fara waka.

Ya kara da cewa cikin irin sakonin da yake isarwa a waka mafi yawa dai sakonnin sun hada da abinda yake faruwa ga al’umma. Ya kuma ce wani lokacin kuma ana duba abubuwan da ke faruwa kusa da mawaki sannan sai mawakin ya wake wannan al’amari .

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:19 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG