Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musa Danjika Ya Shirya Gasar M A 2019 Cup A Jihar Bauchi


A ranar Talata 25/9/2018 ne aka fara wata gasar kwallon kafa ta maigirma gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abdullahi Abubakar mai take Kobi Pre-season MA 2019 Cup, wadda Alhaji Aliyu Musa Dan jika ya dauki nauyin shiryawa a karkashin kwamitin shirya gasa na yankin Kobi dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya (Kobi LOC).

kungiyoyi guda goma sha biyu ne da suka fito daga yankin Kobi zasu fafata a wasannin bisa tsarin kihuwa daya wato ( Nock Out) Kungiyoyin sun hada da;

Voa flamingo,

Sport Supply,

Two Touch,

Golden Soccer,

Golden Flamingo,

Eleven Scorpion,

Samba Gwabba,

Monaco Kobi,

Juventus Fc,

Junior Pepsi, sauran su ne Giwa Academic,

Stationary Stores,

An bude wasan farkon ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta VOA Flamingo Fc dake jihar Bauchi da kuma Sport Supply Fc inda VOA ta samu nasara da ci 2-1.

Babban bako da ya bude gasar shine Alhaji Aliyu Musa Dan Jika (Maji Kiran Turum) a hirar sa da yayi da wakilin dandalinvoa a wajan ya ce an sa sunan Mai girma Gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abdullahi Abubakar, a cin gasar ganin yadda yake bada gudummuwar sa ta cigaba a bangaren wasanni.

Wannan wasa shine karo na farko da aka fara yi a bangaren matasa da ke jihar domin taimakawa wajan ganin cewar matasan sun dogara da kansu kan abinda suka iya musamman ta wannan fannin na kwallon kafa inda ya kara da cewa zasu fadada wasan zuwa sassa shida da ake dasu a garin Bauchi.

Aliyu Musa Danjika, ya ce zasu cigaba da bada shawarwari wa gwamnatin jihar karkashin jagoranci Gwamnatin M A Abubakar don ganin ta kara azama wajan tallafa wa matasa domin su zamo masu dogara da kansu.

Ga yadda hirar sa da Bala Dahiru Bauchi ta kasance

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG