Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Christiano Ronaldo Ya Fita Daga Filin Wasa Yana Kuka


Shahararen dan wasan kwallon kafa na duniya Christiano Ronaldo ya fice daga cikin filin wasa na Estadio Mestalla yana zubda hawaye bayan da alkalin wasa ya bashi jan kati a wasan Juventus da Valencia a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na bana wanda akayi a kasar Spain a lokacin wasan rukuni na farko.

Alkalin wasan Felix Brych ya Sallami Ronaldo ne, mintoci 29 da fara wasan a bayan da suka game da Jeison Murillo mai tsaron bayan Valencia har ta kai ga Cristiano ya kai masa duka a yayin da suke gwagwarmayar daukar kwallon.

Sai Murillo ya fadi kasa, hakan ya ja hankalin alakalin wasa har inda ji ta bakin mataimakin sa, kafin ya koma filn wasai don nunawa Ronaldo jan kati, ya fice daga wasan

Sai dai duk da rashin Cristiano a wasan Juventus din ta doke Valencia daci 2-0

Sakamakon haka dan wasan ba zai buga wasan da Juventus za ta yi Young Boys a ranar 2 ga watan Oktoba ba a wasan rukunin na (H) na biyu ke nan.

Sai dai kungiyar sa ta Juventus tace zata daukaka kara a kan cewar bashi Jan Katin bai dace ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG