Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan tsaron Najeriya ya bayyana manufar taron nukiliya da suke yi


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da ministan tsaron kasar ya rufa masa baya zuwa taron nukuliya
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da ministan tsaron kasar ya rufa masa baya zuwa taron nukuliya

Shugaban Najeriya tare da tawagarsa suna cikin wadanda suke cikin taron nukiliya da ake yi yanzu a Washington DC fadar gwamnatin Amurka

Muryar Amurka ta zanta da ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Muhammad Dan Ali mai ritaya domin bayyana makasudin taron da kuma kasancewar Najeriya duk da cewa kasar bata da makaman nukiliya ko makamashi daga nukiliya.

Batun tsaro da yin anfani da nukiliya ya shafi duk duniya. Yace idan aka bari 'yan ta'ada suka samu nukiliya duniya ta shiga uku dalili ke nan kasashen duniya suka damu.

Akan dalilin da aka gayyaci Najeriya zuwa taron Janar Dan Ali yace rawar da Najeriya ta taka a yaki da 'yan ta'ada ya sa masu shirya taron suka nemi kasancewar kasar saboda ta bada shawarwari akan abun da ta sani akan yadda za'a kawar da 'yan ta'ada.

Akan ko Najeriya zata karu da taron ganin ita kanta bata da nukiliya sai Janar Dan Ali yace kwarai kasar zata karu domin ilimi ne kuma kasar na fatan watarana zata mallaki nukiliya. Yace kada a manta Najeriya tana da kwararru akan ilimin nukiliya kuma suna cikin ayyukanta a wurare daban daban a duniya.

Dangane da yaduwar makamai a Najeriya ministan yace akwai kwamiti akan yaduwar makamai. Akwai kuma masu leken asiri na musamman akan dakile yaduwar makamai. Amma ya kara da cewa umalubaisan yaduwar makamai a Najeriya tarwatsewar kasar Libya ne ya haddasa. Yanzu kasar na shirin kafa abubuwan leken asiri kan iyaokinta da zummar shawo kan lamarin. Bugu da kari ministan yace ma'aikatarsa da ta tsaron cikin gida suna hada karfi da karfe domin yakar yaduwar makamai.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG