Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Da Ya Tashi Lokacin Daukar Fim Na Jackie Chan Ya Razana Mutaned


Shahararren dan wasan fina-finan kareti, Jackie Chan, dan kasar China, da sauran jami'an kamfaninsa dake shirya wani sabon mai suna “The Foreigner” a kasar Ingila, sun firgitar da jama'a da dama, lokacin da suka tayar da wata nakiya cikin wata motar bas, a yayin da suke daukar wannan fim.

An tada bom a cikin wata motar bas mai hawa biyu a dai-dai lokacin da take tafiya akan wata babbar gada mai suna “Lambeth Bridge” duk a cikin kokarin kayatar da fim din.

Tada wannan bam din a cikin motar ya tada ma mutane masu yawon shakatawa hankali, har ma da wasu dake zaune a kusa da wannan gadar, a dalilin tsoro da sukaji bayan tada bom din, duk dai da cewar mutane mazauna kusa da anguwar an ba su takarda da cewar za’a saka wannan bom din mai kara don haka su shirya.

Wannan abun dai yafi shafar mutane baki a wannan yankin, da kuma yara da ke shawagi ko suke gidajen iyayen su a kusa da wannan gadar. Al’uma da dama dai na nuna rashin jin dadin su, da yadda abun ya razuna ‘yayan su, kuma wasu daga ciki sun ta maganganu a shafufukan yanar gizo, kamar su facebook, da twitter.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG