Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man Bilicin Baya Da Tasiri A lokacin Hunturu -Inji Wasu 'yan Mata


A yau wakiliyar dandalin VOA ta samu zantawa da wasu 'yan mata da suka koka da cewar a lokacin sanyi fatar jikinsu bata daukar man shafawa da suke shafawa musamma domin canza launin fatar jikinsu.

A ta bakin 'yan matan, sai su yi ta shafa man shafawar batare da launin fatarsu jiin nasu ta canza ba. Wasu daga cikin 'yan matan sun bayyana cewa dalilian da ke sa suna shafa irin wannan man shafawa dai shine, hasken fata na jawo samari cikin karamin lokaci.

A ci gaba da zantawa da wasu daga cikin 'yan matan, sun bayyana cewar babu abin da zai sa su daina anfani da irin wannan man shafawa mai canza launin fata wanda akak fi sani da man bilicin.

Man bilicin dai kamar yadda kwararrun likitoci suka bayyana, nada matukar illa akan fatar duk wanda ke anfani da shi, kuma yakan haifar da illoli daban ga rayuwar bil'adama.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG