Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gargadi Daga Malama Rahama Muhamed, Hattara dai matasa!


Dangane da sabuwar dabi’ar nan da matasa samari da ‘yan mata ke yi ta wankan yamma da wankan karas, Malama Rahama Muhamed magidanciya ce kuma malama musamman ga ‘yan mata matasa wadanda ke shirin aure, kuma takan ziyar ce su domin yi masu wa’azi da fadakar da su akan al’amurran aure da zamantakewa.

A bayanan da malamar ta yi mana, ta bayyana cewa wannan dabi’a ta wankan yamma da wankan karas da samari ke yi mummunar dabi’a ce domin kuwa a addinance Allah ya haramta yawancin irin ayyukan da matasan ke aikatawa bayan haduwa da juna.

Malamar ta yi kira ga iyaye da su ja ‘ya’yan su mata a jika, sa’annan samarin kuma, a rika ja masu kunne domin duk abin da mutum ya aikata ko bajima ko badade sai an yi masa.

Daga karshe ta ce ‘yanh mata ayi hattara, saboda kuwa yawancin samari masu wankan karas ko wankan yamma baa bin alkhairi suke nema ba.

Saurari cikakkiyar hirar…dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG