Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makaho Baya Bukatar Dan Jagora Da Fasahar Gilashi Mai Gani


An kirkiro wata sabuwar fasaha da zata taimakawa makafi kokuma mutane masu matsalar gani yadda za su aiwatar da harkokin su na yau da kullum ba tare da taimakon wani ba.

Wannan fasaha dai ta hada da wani gilashi ne mai na'urar daukar hoto da kuma wayar hannu wadanda zasu rika ba wanda yake sanye da su damar fahimtar irin wurin da yake da duk wasu abubuwa dake kusa.

Ita dai wannan fasaha zata taimakawa makafi ko marasa gani soasai wajan yi masu jagora a lokacin da suke tafiya, zata kuma bayyana masu abubuwan da ke faruwa a lokacin da ake gudanar da su, bugu da kari wannan fasaha zata iya karanta rubutu domin mai anfani da ita.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG