Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Samari ke cewa A Game Da Mata Masu Kwalliya Da Lalle/Kumshi


Kamar yadda muka tattauna da 'yan mata daban daban domin jin ra'ayin su dangane da tasirin yin kwalliya da lalle/kumshi, a yau mun nemi jin ta bakin samari ne koda shike 'yan matan sun bayyana cewa kwalliyar na matukar jan hankalin samari amma masu iya magana sun ce waka bakin mai ita tafi dadi, ta dalilin haka ne muka ji ra'ayoyin su mabanbanta.

Yin kwalliya da lalle ko kumshi al'adar bahaushe ce dan haka ba bakon abu bane idan mace ta yi kwalliya da shi.

Kamar yadda daya daga cikin samarin da muka ji ta bakin su ya bayyana, malamin ya ce sa lalle na daya daga cikin dabi'un da suke burge shi, harma ya kara da cewa watarana ya yi ma budurwar sa gagarumar kyautar da bai taba tsammani zai iya yi ba sanadiyar kwalliyar da ta yi.

Jama'a da dama sun bayyana ra'ayoyinsu inda har ma wasu daga ciki suka bayyana cewar suna yin iyakacin kokarin su domin ganin cewar sun ba 'yan matan su ko matan su na aure kudi domin gyara jikin su.

Ga cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG