Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Kama Sana'a Mata - Inji Hajiya Bebi Mai Gyaran jiki,


Hajiya Babe Mai Gyaran Jiki
Hajiya Babe Mai Gyaran Jiki

DandalinVOA ya samu zantawa da wata mace hajiya Bebi Mai Gyaran jiki, matashiya kuma matar aure da ke sana'ar gyaran jiki a cikin gidanta Ta ce ita 'yar asali kasar Chadi ce kuma aure ne ya kawo ta Kano kuma hakan bai sa ta zaman banza ba a gida illar kara mata kwarin gwiwa wajen neman nata na kashin kanta.

Ta ce da sana'ar da ta ke yi a yanzu tana biya wa kanta kananan bukatu har da wasu da suka shafi harkokin gidan aurenta na yau da kullum, ta kuma kara da cewar kayan kamshi kamar su turaren wuta, da zannuwa da kwalliyar Amare da sauran abubuwa na mata makamantan su duk ba wanda bata sayar wa.

Hajiyar ta bayyana cewa ta koyi sana'a ne tun tana karama ta ga iyayenta na sana'a, dan haka zaman ta a jahar Kano a cewar ta sai godiya ga Allah.

Shekaru kusan goma sha biyar kenan da fara sana'ar gyaran jiki da turarenn wuta kuma ta ce bata da matsalar komi duk da yawan jama'ar da take hulda su, kuma ta ce a kowace rana takan yima mata sama da bakawi gyaran jiki a kowacev rana.

ku biyu mu domin jin cikakkiyar hirar mu da ita.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG