Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Lefi Ya Kai Kansa Ga ‘Yan Sanda


Near the start of a training exercise for London's emergency services, armed police officers stand near the disused Aldwych underground train station in London, June 30, 2015.
Near the start of a training exercise for London's emergency services, armed police officers stand near the disused Aldwych underground train station in London, June 30, 2015.

Wani matashi mai shekaru 25 da haihuwa kuma mai lefi ya kai kansa ga jami’an tsaro, alokacin da ya nemi aiki a ofishin ‘yan sanda na jihar Michigan dake Amurka. Bayan da ya cike takardar neman aiki ne, aka kuma gudanar da bincike kansa, nan ne aka gano cewa ana nemansa kan aikata laifin fyade a jihar Kentucky.

Jami’an sandan sunce sun cafke matashin mai suna John Wesley Rose, kuma za’a mayar da shi jihar da ya aikata wannan laifi, inda ake nemansa kan laifukan fyade har shida.

An dai kama matashin ne ranar Talata bayan kammala binciken da ma’aikatan tsaro keyi kafin su ‘daukar ma’aikata, nan ne aka gano cewa akwai sammaci kansa ana neman sa ruwa a jallo tun watan Maris.

Ofishin ‘yan sandan dai sun yiwa Rose wayo inda suka bukace shi da ya kai musu duk takardun da ya cike yanke hukuncin bashi aiki, alokacin da ya kai musu ne suka cafke shi ba tare da wata rigima ba.

XS
SM
MD
LG