Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lokacin Damawa Da Mata A Kannywood Yayi


Rashida Adam Abdullahi Mai Sa'a
Rashida Adam Abdullahi Mai Sa'a

An bukaci mata dasu dukufa wajan harkokin siyasar kungiyar fina fina ta Kannywood, mai baiwa Gwamnan jihar Kano shawara akan harkokin mata Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, ne ta furta haka a hirarsu da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir.
Ta kara da cewa dalilin da ya sa ta fito takara shine domin lokaci yayi da mata suma zasu fito a dama dasu tana mai cewa mace it ace tushen tarbiya, inda tarbiya ta yi kyau sai da taimakon mace haka idan aka samu akasi ta kara da cewa ta lura da lokaci yayi da za’a dama da mata kamar kowa.

Rashida ta ce akwai karanci damawa da mata a masana’antar Kannywood wanda hakan ya karanata kwarin gwiwar fitowa domin a dama da ita, kwatsam an kusa gudanar da zabe sai hukumar SSS ta tsayar da zaben.

Tace dakatar da zaben shugabanci masu shirya fina-finan ta jihar Kano sakamakon korafi da aka kaiwa jami’an tsaro ba zai hana kungiyar ci gaba ba.

Ta ce kawo yanzu rundunar yan sandan Jihar Kano na gudanar da bincike duk da cewar hukumar tace fina-finan na zargin cewar kungiyar bata da rijista amma binciken ‘yan Sanda zai tabbatar da gaskiyar alamarin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG