Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lokaci Da Wadanda Suka Kamata A Ba Zakkar Fiddakai


Da yake an shiga goma ta karshe wadda Bahaushe ke cewa goma ta dokin sallah, a yau DandalinVOA ya duba batun nan na Zakatul fitr, da malan Ahmad Tijjani Mijinyawa, dangane da menene zakatul fitr, da kuma lokacin da ya kamata a fitar da ita.

Malan Ahmad Tijjani, ya ce Zakatul fitr, zakka ce da ake yinta bayan anyi fitiri wato an kammala azumin watan Ramadan ga dukkanin wadanda suke da iko, kuma sunna ce ga dukkanin masu hali mussaman masu hannu da shuni.

Ya ce Zakatul fitr, ta rataya a kan magidanta da ma wadanda basu da aure, walau mace ko namiji domin a taimakawa marasa karfi tare da baiwa mabukata karfin fita sallar idi cikin nishadi da walwala.

Ya kara da cewar idan mutun shi kadai ne an so ya dafa abinci ya bayar da dafaffe, kuma a safiyar sallah domin a saukakawa mabukata don samun nishadi kamar kowa, kuma ana awon hatsi ne domin fitar da Zakatul fitr, da ma'auni da ake cewa muddunabi.

Mal Tijjani Mijinyawa, ya kara da cewa ana bada Zakatul fitr, ne da nau’ukan abinci da wannan yanki ke ci, kuma ana fitar da ita ne iya adadin mutanen da suke karkashin wanda zai fitar da ita.

Daga cikin rukunin mutanen da ya kamata a baiwa zakatul fitr dai sun hada da masu rauni, wadanda basu da cin yau ko na gobe mussaman ma marayu da ma gajiyayyu.

Daga cikin alfanun dake cikin zakatul fitr sun hada da bin umarnin Allah ta'ala, tare da samun ladar ciyarwa a wata ramadan, domin yana jawo arziki tsakanin kai da ka bayar da wanda ka ba yana kuma jawo karuwar arziki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG