Dan wasan gaba kana kaftin a tawagar kungiyar kwallon kafar kasar Argentina, wanda yake taka leda a Kulob din Barcelona Lionel Messi, zai koma buga wa kasar tasa tamola a karon farko tun bayan gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a shekarar 2018.
Ta bakin Kocin Argentina, Lionel Scaloni ya bayyana da cewar watakila Messi zai buga wa Argentina daya daga cikin wasan sada zumunta, da za ta yi da Venezuela ko kuma Morocco cikin watan nan da muke ciki.
Messi ya shafe watanni da dama bai buga wa kasar Argentina wasa ba, bayan da aka fitar dasu a gasar cin kofin duniya inda Faransa ta doketa a zagaye na biyu a gasar.
Shahararren dan wasan Messi shi ne ke kan gaba wajen yawan zura kwallaye a raga a kungiyar ta kasar Argentina inda yaci 65, duk da irin kokarinsa Messi yana shan suka, cewar kokarin da yake yi a Barcelona ba ya yin irinsa ga kungiyar kwallon kafar kasar shi.
Facebook Forum