Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar 'Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Arsenal Ta Lallasa Takwararta


‘Yan wasan kungiyar Arsenal sun kasance su goma kacal a filin wasa kamin suka sami nasarar yin kunnen doki a lokacin da dan wasan ta Theo Walcott ya jefa kwallo a raga.

Kungiyar ta Arsenal ta lallasa takwararta Leicester City da ci biyu da daya ne a filin wasa na Emirates, wanda ya daga kungiyar da maki biyu da ke kan gaba a wasannin zakarun turai.

Jamie Vardy ne ya murda kwallon a yayin da ya yi bugun daga kai sai mai tsaron gida daf da hutun rabin lokaci, inda aka fitar da dan wasan, kuma hakan ya canza yanayin wasan.

Wasan ya canza a yayin da kungiyar ‘yan wasan ta Gunners ta sami canjin dan wasa guda wato Theo Walcot wanda ya jefa kwallo ta biyu cikin mintuna 20 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kulob din na Aresnal ya sami darewa kan gaba a rukunin, kafin haduwar kungiyar Manchester City da Tottenham.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG