Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Fortuna Ta Kori Sunday Oliseh A Matsayin Kocin Ta


A yau laraba ne kungiyar kwallon kafa ta Fortuna Sittard, ta fitar da sanarwa a shafinta na yanar gizo ta korar tsahon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle, kuma tsaohon kocin kungiyar Sunday Oliseh, a matsayin kocin kungiyar.

Kungiyar ta bayyana cewa babu jituwa mai kyau tsakanin kocin da sauran jiga jigan kungiyar bayan haka kuma ya haifar da rashin dangantaka tsakanin ‘yan wasan da shugabannin su. Mujallar Daily post ta wallafa cewa bayanan da kungiyar ta fitar a shafin ta na yanar gizo ya bayyana cewa;

“kwamitin gudanarwa na kungiyar ya yanke hukunci akan yawaita aikata laifuka na loakci mai tsawo da mai horas da ‘yan wasan ya dade yana yi”

“kungiyar ta dade tana kokari domin ganin cewa ya sauya halin sa amma haka bata cimma ruwa ba, babu dangantaka mai kyau tsakanin mai horas da ‘yan wasan da ‘yan wasan kungiyar da sauran shugabannin ta”.

Oliseh, dai ya jagoranci kungiyar Fortuna, daga farkon kakar wasanni ta bara, zuwa yanzu.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG