Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Wasu Sauye Sauye A Firimiya Lig


Hukumar dake Shirya Lig lig na tarayyar Najeriya LMC ta fitar da wasu sauye-sauye a jaddawalin wasannin Firimiya lig saboda wasan CAF da wasu kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya zasuyi a watan nan na Fabareru.

A cikin wata sanarwa daga hukumar ta LMC mai dauke da Sanya hannu babban jami'in harkokin gudanarwa, Salihu Abubakar, ta bayyana wasannin da aka samu sauye sayen kamar haka.

Wikki Tourists da Lobi Stars daga 11/02/18 zuwa 12/02/18, Enyimba da Plateau United daga 11/02/18 Zuwa Laraba 14/02/18, MFM da Akwa United 11/02/18 Zuwa 28/02/18.

Sauran wasannin da aka canja musu rana sun hada da wasan Akwa United da Heartland daga ranar 25/02/18 zuwa 07/03/18, Go Round da Plateau United 25/02/18 zuwa 28/02/18 sai kuma na MFM da Lobi Stars 25/02/18 zuwa 07/03/18.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG