Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Jihar Kano Ta Tuhumi Matashin Da Ya Yiwa Kananan Yara Maza Su 4 Fyade


Kotun majistire dake a Audu Bako Sakatariya a jihar Kano ta tsare wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa mai suna Aliyu Muhammed bisa zarginsa da akai da aikata laifin yin lalata da kananan yara maza.

Rahotanni sun bayyana cewa Muhammad yana kai kananan yaran dakinsa ne inda yake aikata wannan mummunan abu dasu.

Mujallar Daily post ta wallafa cewa mai gabatar da karar Asp. Rufa’I Inusa, ya bayyanawa kotun cewar Ado Mu’azu, da Musa Nura, da Mati Isa ne suka kai karar Aliyu Muhammad a ofishin ‘yan sanda dake karamar hukumar Bichi dake jihar kano ranar 5, ga watan Nuwambar shekarar data gabata, amma daga nan aka garzaya da yaran zuwa asibitin karamar hukumar Bichi.

Kotun ta tuhumi matasahin da aikata laifukan da ba’a saba ganiba a al’adance wanda ke da hukunci a karkashin sashi na 284, na Penal Code, duk da haka wanda ake tuhumar ya musanta zargin.

Mai shari’a Muhammad Jibril, ya dage sharia’ar kuma ya bada umurnin a cigaba da tsare wanda ake zargi da aikata laifin a gidan kaso har ranar 9, ga watan fabarairu

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG