Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Mai Yankan Kai Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Wani matashi Musiliu Taheed, mai shekaru talatin ya tsallake rijiya da baya a lokacin da matasa suka yi masa duka baya da aka kamashi da kan mutune a unguwar Olomi, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shi dai wanna matashi, yana tone gawa daga kabari baya a binne gawar a makabarta, yana yanke kan mamaci domin aikita tsafe tsafe, mutanen unguwar sun dade suna fakonsa wannan matashi mai muguwar dabia’r yanke kawunnan mamata.

Da mutanen unguwar suka damke shi sun nakadamashi duka na fitar rai, amma jami’an rundunar ‘yan Sandan jihar, ne suka shiga tsakanin suka hanna matasan su kasha shi.

Kakakin rundunar ‘yan jihar Oyo Adekunle Ajisebutu, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a lokacin da ya nuna Musiliu, ga manema labarai yace sai da ruindunar ta karo Karin jami’a, kafin su sha kafin matasan dake kokarin hallaka Wannan matashi Musiliu.

Shi kuwa matashi da ake masa tambayoyi yace yana kaiwa masu masu bukata domin yin maganin kudi ne, kuma a cewarsa wanna shine karo na biyu.

XS
SM
MD
LG