Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayyade Yawan Mu'amulla Da Kudi Da Babban Bankin CBN Ke Shirin Yi Zai Shafi 'Yan kasuwa


Wato shi tsarin tattalin arzikin kasa a cewar Malam Lawan Habibu Yahaya, shugaba a fannin bankuna da harkokin kudi na makarantar gaba da sakandire, Kano Polytechnic yayin da yake bayani akan sabon shirin da babban bankin Najeriya CBN ke kokarin kaddamarwa na kayyade yawan kudin da ‘yan kasuwa da sauran jama’a zasu iya cirewa daga asusun ajiyar su na banki, abu ne da yake bukatar natsuwa da duba yadda tattalin arzikin kasa kacokan yake.

Kafin aikin banki ya sami nasarar rage yawan kudi da ake hada hadar yau da kullum kamar yadda kasashen da suka ci gaba suke yi, wato amfani da katin cire kudi irin na ATM wajan saye da sayarwa, da kuma amfani da shafukan yanar gizo wajan aiwatar da harkokin kasuwanci, dole sai kasar da wadannan bankuna suke ta sami damar samar da abubuwa da dama.

Na farko dole ne kasa ta iya samar da Network mai inganci, da kayayyakin da ake bukata kamar su wutar lantarki da sauransu domin a cewar sababu yadda za’a iya cimma irin wannan manufa ba tare da abubuwan da ya lissafa ba.

Shekaru kadan da suka gabata ne kasashen da suka ci gaba suka kaddamar da irin wannan hanya ta amfani da katin ATM wajan cinikayya da kuma yanar gizo, kuma hakan ya taimaka masu wajan rage yawan kudaden da ke hannun jama’a, kuma lallai sun sami nasarar rage yawan kudin da kowane mutum ka iya fiddawa daga asusun ajiyar san a banki.

Wannan tsari ne mai kyau domin kuwa ya rage yawan barayi, da kuma kudaden da ake kashewa wajan sake buga takardun kudin da sauran abubuwa da dama.

Sai dai babbar matsalar a cewar sa it ace, idan babban bankin Najeriya ya kayyade yawan kudin da kowa zai iya fitarwa a rana zuwa Naira dubu goma, babu shakka zai shafi rayuwar jama’a da dama musamman ‘yan kasuwa domin kuwa dubu goma tamkar kudin cefane ce a wurin wasu, yaya ‘yan kasuwa zasu yi?, wannan zai shafi al’umma da kuma tattalin arzikin kasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG