Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kankana Ta Taimaka Wajen Tantance Masu Kada Kuri’a


Kankana ma da ranarta
Kankana ma da ranarta

A wani al'amari mai ban sha'awa da mamaki, kankana ta taimaka da wanke hannaye masu kaushi da tauri ko kuma dauda, har na'urar tantance masu kada kuri'a ta iya tantancewa

Lashakka jama’a na jinsoshi daban-daban sun taimaka wajen gudanar da zaben Najeriya. To amma kankana ma, wace ba mutum ba ce, ta taimaka gaya, inda ta yi ta wanke hannaye masu dauda ko tauri da kaushi, har na’urar nasara ta iya tantance masu kada kuri’a wadanda a baya ta kasa tantance su.

Wakiliyarmu Baraka Bashir ta aiko da rahoton yadda kankana ta yi ta taimakawa a Karamar Hukumar Kura, wacen sa hannaye masu dauda ko tauri ko kaushi su yi laushin da na’urar tantancewa ke bukata don ta iya tantancewar. Wani jami’in zabe mai suna Malam Babu Kura Kofar Gabas ya tattabar ma Baraka cewa suna amfani da kankana idan na’ura ta kasa tantance hannu saboda takan wanke tare da lausasa irin wadannan hannayen. Haka zalika wani mai kada kuri’a mai suna Abubakar Idrisa ya tabbatar cewa kankanar na taimakawa, kamar yadda wani mai suna Dan’auta Salihu Kura ya tabbatar. Haka zalika wani jami’in zabe na mazabar Tanawa mai suna Yakasai ya tabbatar da taimakawar da kankanar ke yi. Ya ce ya ga mutane akalla 20 da kankanar ta taimaka masu.

Baya ga wannan abin ban sha’awa na amfani da kankana, wani kuma abin da ya burge mutane shi ne yadda nakasassu su ka fito gadan-gadan su ka kada kuri’unsu. Baraka ta ruwaito wani nakasasshe a Karamar Hukumar Dawakin Kudu mai suna Badamasi Dawakin Kudu na cewa mai masa jagora ne ya kai shi wurin zaben. Haka shi ma Sarkin Guragun Karamar Hukumar Dawakin Kudu y ace ya je ya kada kuri’arsa cikin azama. Shi ma Ciyaman din Guragu na Karamar Hukumar Dawakin Kudu Abubakar Suleiman ya ce lallai tsarin da hukumar zabe ta yi na kare nakasassu masu kada kuri’a ya yi kyau, saboda cikin sauki ya kada kuri’arsa.

XS
SM
MD
LG