Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanen Wata Jarumar Nollywood Ya Yi Mata Duka


Jarumar fina finan Nollywood Joju Muse ta yi kira ga hukumomi da su dauki kwararan matakan hukumtaa masu cin zarafin mata, tayi wannan kira ne a sakamakon dukan da wani kanen ta mai shekaru goma sha tara da haihuwa yayi mata akan wata ‘yar gardama da ta shiga tsakanin su.

Jarumar da aka fi sani da lakabin April ta wallafa hotunan dake nuna irin dukan da kanen nata yayi mata a shafin ta na facebook ne ranar 22 ga wannan watan da muke ciki na Mayu, wanda yayi sanadiyyar bukatar daukan hoton xray domin a bincika ko ta sami rauni a cikin kirjin ta.

A cewar ta, cin zarafin ya samo asali ne a dalilin fadawa kanen nata cewa ya yi wanke wanken kwanonin da aka ci abinci da su, ta ce “daga na fada masa ya wanke kwanonin da ya ci abinci ya bari tun ranar juma’a kafin ya koma makaranta ranar lahadi” kamar yadda ta rubuta a shafin nata inda jama’a da dama suke cigaba da tausaya mata, wasu kuma suka kalubalance ta da wallafa lamarin da ya shfi iyalin ta a akan shafin yanar gizo.

Jarumar ta ce tayi hakanne domin ta gyara halayen dan’uwan nata wanda yakamata ya kare hakkin matar sa nan gaba a maimakon dukan ta. Ta kara da cewa idan wulakanta kaina ta shafin facebook zai sa kanena ya sami makoma mai kyau.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG