Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Mai Bukatar Kwakwalwar Yara A Jikin Tsufa?


Daya daga cikin hanyoyi sama da dubu da mutun zai iya magance matsalar mantuwa a yayi tsufa shine. Tsayawa kan hadahdar yau da kullun na amfanada da bunkasar kwakwalwa, tun a yarunta da shekarun tsufa.

Likitoci masu bincike sun bayyanar da cewar idan mutun yana yawaita amfani da kwakwalwar shi wajen tunani mai amfani da karance karance masu amfani, haka da buga wasannani da zasu saka mutun yin amfani da nazari wajen warware wata matsala na taiamakawa matuka.

A cikin mutane dari ukku 300, da suka shiga cikin wani bincike da aka gudanar, na wata hukuma “Dallas Lifespan Brain Study” mai binciken ya bayyanar da cewar cikin manyan mutane da suke da shekaru hamsin 50, wadanda suke amfani da kwakwalwar su sun fi nagartacciyar lafiya da kuzari.

Suna da kaifin basira da rike abubuwa masu yawa a cikin kwakwalwar su, sanadiyyar kokarin da sukeyi na tunani mai amfani a kowane lokaci. Su kuwa wadanda ke da shekaru sama da tamani da tara 89, sukan fuskanci matsalar mantuwa da rashin karfin jiki. A takaice rahoton na nuni da cewar idan mutun yana amfani da nazari wajen warware matsalolin da suke shigama al’uma duhu to ba shakka zai samu lafiya mai nagarta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG