Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaruman Masana’antar Fina-finai A Harkokin Zabe


Kabiru Musa Janmaje Da Balarabe Murtala
Kabiru Musa Janmaje Da Balarabe Murtala

Yayin da babban zaben Najeriya ke karatowa, lokaci ne da a duk duniyar harkokin fina-finai akan samu wasu daga cikin jarumai na fitowa domin nuna jam’iyyar da suke muradi ta hanyar fitowa fili da bayyana wanda suke goyawa baya.

A Najeriya ma haka lamarin yak e, inda wasu lokuta ma har ta kai ga cewar wasu jarumai na fitowa fili domin nuna wanda suke so ba tare da bukatar masoyansu da su zabe wanda suke so.

Duk kuwa da cewar hakan ba dai-dai ba ne ga wannan dabi’a ta wasu jarumai da suka yi fice, kamar yadda Murtala Balarabe Baharu, ke fadi a yayin zantawa da wakiliyar Dandalin VOA, tare da cewar ba wani abu ne mara kyau ba, dan wani jarumi ya tsunduma ga harka ta siyasa, ko bukatar wani jarumi da ya mara wani dan siyasa baya a lokacin zabe .

Amma babban abin dubawa a ta bakin Bahuru dai shi ne jarumi ya lura da cancanta tare da ‘kauracewa fitowa fili domin nuna jamiyyar su ga masoyansu.

Baharu, ya kara da cewa wasu daga cikin dalilan da masu shirya fina-finai da jarumai ke shiga harkar siyasa watakila yana da nasaba ne da yadda ake samun karanci hada-hada na kasuwancin fina-finansu tare da rashin samun kasuwa a gidajen talabijin na fina-finan su.

Shi kuwa Kabiru Jammaje, ya amince da abin da takwaransa ya fada a baya inda yake cewa, a yanzu da zarar an saki fim kafin a samu mutum daya da zai saye original an zubawa dubu ta hanyar turawa a wayoyin alumma ko ta hanyar buga su a faifen CD.

Ya kara da cewa akwai dalilan daban-daban da suka haddasa kasuwar fina-finai ta yi kasa sannan duk duniya harkar fim sana’a ce mai zaman kanta da take neman kirkira da jajircewa sabanin yadda abubuwa ke wakana a yanzu.

Daga karshe Baharu, ya ce ya kamata masu shirya fina-finai da su fito da wasu hanyoyin inganta Kannywood tare da kauracewa jiran sai gwamnati ta yi musu wani abu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG