Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Shigar Mu Ta Ringa Nuna Asalinmu: Malam Khalid Musa


Ya Kamata Shigar Mu Ta Dunga Nuna Asalinmu:Malam Khalid Musa

Khalid Musa - Marubuci, kuma mai shirya fina-finai wanda ya shafe shekaru Talatin da suka wuce ya na harkar fina-finai, ya ce harkar fim ta zama wata babbar kasuwanci sabanin yadda take a da.

A cewar Khalid mafi akasari wadanda suke harkar fina-finai ba sa mai da hankali ko tunanin masana’antar za ta zama babbar kasuwa ba.

Ya ci gaba da cewa babbar sharawa ga masu shirya fina-finai itace ya kamata su dinga gudanar da bincike kafin su fitar da kowanne irin fim ne, sannan masu zuba kudadensu domin shirya fina-fanai, wajibi ne su nemi furodusan da ya san abin da yake yi, ya kuma san ka’idojin da ake bi kafin a fitar da labari har ta kai ga fitar da fim.

Ya ce labarin fim ya bambanta da labaran littafi, tsarin yadda ake rubuta kowanne yana da bambanci, a don haka ne yake da alfanu masu shiryawa su yi nazari sannan su ma marubuta ya na da muhimmancin su yi bincike a kowanne labarin da zasu rubuta sannan dole su dinga yawan kallon fina-finai.

Yadda ake tsara labari a da, da na yanzu akwai bambanci domin ada labaran suna da karfi sabanin a yanzu, mafi yawan wadanda suke rubuta labaran fim a da marubuta ne kuma suna mai da hankali ne ga yadda malam Bahaushe ya ke zaune da kuma yanayin zamantakewarsa.

Labarai a yanzu mafi yawan lokuta ba marubuta ba ne suke rubuta su, sannan akan nuno fim, jaruman da za’a gansu da shiga ba irin ta malama Bahaushe amma labarin da fim din ya kunsa ba ta kasar Hausa ba ce.

Masana’antar Kannywood tana da karancin marubuta ko kuma masu shirya fina-finai ne suke da karancin masaniya akan mene ne fim ko kuma ya na kasalar bincike kafin ya fitar da labari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:13 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG