Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Na Shirin Gwajin Mota Mai Tashi Sama


Gwamnatin Japan ita take daukan nauyi wannan mototcin masu tashi sama, da take da burin ta ga mutane sun fara amfani da su zuwa shekarar 2030.

Wani kamfanin kasar Japan mai yin kayan lantarki mai suna NEC Corp., ya nuna wata “Mota mai tashi sama,” - wani katoton jirgi mara matuki da yake kama da inji da yake da fukafuki hudu da ya tashi ya tsaya har tsahon kimanin minti daya.

Gwajin an yi shi ne har na tsawon mita 3 a jiya Litinin, wanda aka rike shi a cikin wani keji na musamman, yayin da ake duba matakan kiyayewa na kariyarsa, a cikin kamfanin NEC Corp. da yake wajen birnin Tokyo.

Ana ta shirye-shirye inda ake ta sake duba inji da kuma yi wa manema labarai gargadi da su saka hular kwano don su samu karin wani lokaci akan gwaje-gwaje da aka yi a takaice guda biyu.

Gwamnatin Japan ita take daukan nauyi wannan mototcin masu tashi sama, da take da burin ta ga mutane sun fara amfani da su nan da zuwa shekarar 2030.

A shekarar 2011 gwamnatin Japan ta goyi bayan wani gagarumin shirin gwada motoci masu tashi da kansu da aka kera a yankin da bala'in Tsunami, ya auku har ya daidaita tashar Fukushima da ke arewa maso gabashin Japan.

Sai dai makamancin irin wadannan ayyukan ana iya ganinsu a sauran kasashen duniya, kamar jirgin Uber a kasar Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG