Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jadawalin Gasar Firimiyar Kasar Ingila Na 2019-2020


An fitar da jadawalin gasar Firimiya na kasar Ingila a kakar wasan 2019-2020. Za a bude gasar ne a ranar Juma'a 9 ga watan Agustar 2019, inda kungiyar Liverpool za ta kece raini tsakaninta da Norwich City wacce a wannan shekarar ta dawo gasar Firimiya a bana, bayan lashe gasar Championship na shekarar da ta gabata.

Ita kuwa kungiyar kwallo ta Manchester United wacce ta kare a matsayi na shida a Firimiyar bara, za ta karbi bakoncin abokiyar hamayyatar Chelsea a ranar Lahadi 11 ga watan Agusta 2019.

Manchester City dake rike da kambun gasar za su fara na su wasan ne da West Ham United.

Aston Villa da Sheffield United, wadanda duka sabbi ne a gasar, za su fafata da Tottenham da kuma Bournemouth.

Arsenal, wacce ta kare a mataki na biyar a kakar da ta gabata, za ta yi tattaki ne zuwa Newcastle domin buga wasanta na farko. Inda yanzu ko wace kungiya ta dukufa don ganin ta sayo sabbin 'yan wasa da zasu taimaka wa kulod din a kakar wasa ta bana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG