Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ingila: Rooney Na Shirin Komawa Derby County


Klab din Derby County yana da kwarin gwiwar kulla wannan yarjejeniya don dakko tsohon Kyaftin England, Wayne Rooney, a yau Talata, acewar mai kulab din Mel Morris.

Yanzu haka dan wasa gaba na kungiyar DC United yana shirin komawa buga kwallo a England a bangaren gasar Championship.

Klub din Derby County yana da kwarin gwiwar kulla wannan yarjejeniya don dakko tsohon Kyaftin Ingila, Wayne Rooney, a yau Talata, a cewar mai klub din Mel Morris.

Wayne Rooney dan shekaru 33 da haihuwa, da gaske yana tunanin yiwuwar ya koma England, kuma dan wasan gaban yanzu haka ana tunani zai ba da mamaki wajen komawarsa buga kwallo a Ingila da ake tsammanin zai zama dan wasa kuma mai horarwa a kungiyar.

A cewar wasu rahotanni, tsaohon dan wasan gaba na Everton da Manchester United za a iya ganinsa a wannan kakar wasannin ta MLS da ake bugawa a Amurka da Canada a kungiyar ta DC United kafin ya koma zuwa Pride Park a watan Janairu mai zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG