Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Inganta Illimin Kimiyyar Na'ura Mai Kwakwalwa


Wayoyin salula da kananan na’urori masu kwakwalwa sun zame mana abin amfani nayau da kullum ga yara harma da matasan mu, amma tunanin yaran ko matasan na kirkirar wasu kayayyakin fasahar na komawa baya.

Dalilin hakane fadar shugaban kasar Amurka ke kokarin canza wannan hanyar da aka dosa, fadar shugaban dai ta bayyana aniyarta na fito da wani shiri ga makarantun Amurka inda zasu ke koyar da kimiyyar na'urar kwamfuta ga duk ‘dalibai.

Wannan shiri zai mai da hakali ne akan yara mata da maza, domin inganta hanyoyin samun aikin fasaha ga zamani mai zuwa. Akan wannan shiri ne shugaban kasar Amurka Barack Obama da mataimakinsa Joe Biden suka hadu da wasu ‘yan makarantar firamare a wani zama na awa daya da kamfanin fasaha na Code.org ya shirya.

a wannan zamane wata yarinya ta nunawa shugaban kasa yadda zai zana siffofi a kwamfuta tayin amfani da nambobin da ake amfani dasu wajen kirkirar manhajar na’urori masu kwakwalwa. Shugaba Obama ya fadi cewa yana da kyau daliban sukoyi yadda ake kera ire-iren yakan fasaha bawai kawai koyar wanda aka riga aka keraba.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG