Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Microsoft Zata Fito da Sabuwar Manhajar Window 10


Microsoft
Microsoft

Kamfanin Fasaha na Microsoft dake kirkirar manhajar nau’rori masu kwakwalwa, wadda suka hada da kwamfutoci har ma da wayoyin hannu.

A baya bayan nan dai kamfanin ya baiwa kowa kunya a fadin duniya, dalilin fitowa da sabuwar manhajar window 8 wadda ke rikita masu amfani da ita harma dasu kansu kamfanin Microsoft din.

Amma yanzu da’alamu kamfanin na yunkurin wanke kansa da wata sabuwar manhajar da zai fitar mai suna window 10.

Kamfanin dai zai yi nunin wannan sabuwar manhajar a karshen wata maizuwa, inda zai bayyana wa mutane abubuwan dake kunshe da wanna sabuwar manhajar kuma zai mayar da hankali kan yadda sabuwar manhajar zata taimaka wajen habbaka aiyukan masu amfani da ita.

Manhajar dai zata zama dandali daya ga duk na’urori masu kwakwalwa wanda ya hada da kwamfutoci, wayar hannu da dai sauransu.

Microsoft dai bai fadi ranar da manhajar zata fito kasuwa ba amma ana kyautata tsammanin za’a fitar da ita a cikin shekara mai zuwa ta 2015.

Microsoft 1'00"
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00

XS
SM
MD
LG