Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Tasirin Lalle/Kumshi Ga Mata?


A wannan makon dandalinvoa ya sami zantawa ne da ‘yan mata matasa domin jin ra’ayoyin su dangane da tasirin amfani kokuma yin kwalliya da lalle kokuma kumshi, wato yadda suke yin zane iri iri a hannuwa da kafafun su mai launin baki ko mai launin ja.

Koda shike yawancin mutane suna alakanta kwalliyar da jan ra’ayin samari, kokuma daukar hankalin mai gida ga matar aure, kwaliya da lalle/kumshi dadaddiyar al’ada ce ga al’umar Hausawa, ganin yadda ko daurin aure za’a yi daya daga cikin kwalliyar da ake ma amaryar shine yi mata kawalliya da lalle ko kumshi.

‘Yan mata musamman na wannan zamani nada hanyoyi daban daban na yin kwalliyar a maimakon yadda ake yi da farko. Daya daga cikin ‘yan matan da dandalin voa ya zanta da su ta ce saurayinta kan yi mata kyauta saboda irin shi’awar kwalliyar da take yi da lalle ko kumshi.

Tasirin sa kamar yadda yawancin ‘yan matan suka bayyana a takaice shine kamar yadda masu iya Magana suka ce idan kana da kyau ka kara da wanka, lalle ko kumshi yakan sa mace ta kara zama mai kwarjini ga sauranyin ta ko mijin ta.

Saurari cikakkiyar hirar

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG