Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hazikin Matashin Mawaki Mai Tarbiya : In Ji Hani Billy O


Lil Ameer Mawaki
Lil Ameer Mawaki

An yi rashin matashin mawaki mai tashe ga tarbiya mai baiwa kowa girmansa in ji Hani Billy O,babban abokin Lil Ameer, in da yake cewa mutane da dama na tsanmanin tare da Lil Ameer suka fadi a kan mashin.

Ya bayyana haka ne a yayin wata hira da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir inda yake cewa hakika mutuwar Lil Ameer, ta shige shi sosai domin kuwa kaninsa ya rasu da kwanaki 56 sai mahaifiyarta ita ma ta rasu, sannan baya tare da ragowan ‘yan uwansa mata suna wajen ‘yan uwansu sai ga kuma mutuwar amininsa in ji Hani- Billy O.

Lil Ameer yayi tasiri a rayuwata inji Hani-Billy O, domin duk wanda yayi ma’amala da shi zai ce yana da hankali da tarbiyya, inda yake mika ta’aziyyarsa ga masoya tare da fatan mai adaidaitan da ya kade Lil Ameer, da ya ji tsoron Allah ya bayyana kansa ya kuma sani cewa azumi da biyan diya ya rataya a wuyansa.

Saboda mutuwar ya ce ya rerawa abokinsa waka, inda yake bayyana cewa shi Kenan Ameer mun rabu? Ba zamu sake haduwa ba?

Muhammad Sani – Elin boy mai rubutawa Lil Ameer waka shima ya ce lallai anyi babban rashi hazikin mawaki yaro, a cewarsa yaro ne mai kwazo da tarbiya da arewa ta yi babban rashinsa.

Musbahu Suleman MSK daraktar marigayi Lil Ameer ya ce zamansa da marigayin zama ne na dadi da fahimtar juna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:44 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG