Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harira Mai Gurasa: Na Kan Kwaba Buhu Biyu Zuwa Biyar Na Fulawa A Kowace Rana


A shirinmu na masu kananan sana’oi a yau DandalinVOA ya samu bakuncin malama Harira Muhammad, wacce ta shafe shekaru 15 tana sana’ar kwabin gurasa da gasa ta inda ta ce tana kwaba kimanin buhu biyar a rana.

Ta ce tana kwaba buhu biyu zuwa biyar na fulawa a duk rana, ta kuma gasa domin kaiwa garuruwan da ke kusa da su ta sayar tare da samun riba daidai kima.

Harira ta ce sana’ar hannu sana’a ce da duk mace mai boko da mara boko ya kamata su runguma, domin a cewarta da sana’ar ne ta dogara.

Daga karshe ta bayyana cewa babu sana’ar da bata da kalubale illa dai kawai mata su jajirce inda ta ce kwatsam wata rana zaka sami mutumin da baya sonka ba gaira babu dalili.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG