Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasahar 5G Na Gab Da Fara Aiki Dan Inganta Rayuwa


Yayin tsarin sadarwa na wayoyin hannu na 5G, na gab da shigowa cikin sauri fiye da yadda mutane ke tsammani, sai dai a wani bangare wannan tsari ya dan so ya fuskantar tafiyar hawainiya.

A shekarar data gabata, jawabin da shugaban kungiyar kamfanonin kasuwancin wayoyin hannu Mr Attwell Baker, ya yi a taron kamfanonin wayoyin hannu cikin watan satumba, babu shakka wannan tsari na 5G, zai inganta rayuwar al’umma.

Amma koda shike yanzu wannan yunkuri ya dan sami jinkiri, fasahar 5G, zata kasance wata gagarumar nasara ga fasahar wayoyin hannu, a cewar shugaba mai bada shawara a fanning gyare – gyare na kamfani wayar hannu na T-Mobile, Mr Naville Ray, a babban taron kamfanonin wayar hannu na duniya na shekarar 2018.

Koda shike fasahar 5G, zata inganta da habaka sauke hotuna, ko bidiyo akan waya cikin hanzari fiye da fasahar 4G, amma bazata maye gurbin 4G, ba kamar yadda 4G, ta kawar da 3G cikin sauri, amma kafin a fara amfani da ita a wayoyin hannu, sai an fara amfani da wannan fasaha a manyan kayan sadarwa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG